Labarai Siyasa

Ana min barazana don naki aminta da takarar Atiku shi kadai a 2023 – Shugaban amintattun PDP

Shugaban kwamitin amintattun jami’iyyar PDP na kasa, Walid Jibrin, ya bayyana yacce ake yi masa barazana domin yaki ambatar Atiku Abubakar a matsayin wanda zaiyi takarar PDP a 2023.

Jibrin, ya bayyana haka ne yayin da yayi taron manema labarai a ranar Alhamis a gidanshi dake jihar Kaduna kamar yacce sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito.

Walid ya bayyana cewa nan da wani dan lokacin kankani, jami’iyyar PDP zata bayyana tsarin da zata bi wajen fito da dan takarar shugabancin Najeriya na zaben 2023.

DABO FM ta tattaro Walid Jibrin, ya tabbatar da cewa dan takarar shugabancin kasa a jami’iyyar zai iya fitowa daga kowanne yankin Najeriya.

Walid ya bayyana cewa ake kirashi a waya tare da yi masa barazana akan yaki aminta da fito da dan yankin Arewa maso gabashin Najeriya a matsayin dan takarar jami’iyyar a 2023.

“Na samu kira daga wasu mutane da suke yimin barazana saboda naki cewa yankin Arewa maso Gabas za’a baiwa takarar kujerar shugaban kasa.”

“Sun ce ni mara kishi ne, kamata yayi in bayyanawa duniya cewa; Atiku Abubakar ne dan takarar PDP daya tilo.”

“Sun ce na fandare, kuma idan ban dawo kan tafarkinsu ba, zasu shirya yan bindiga su kashe ni duk inda naje.”

“Sai na fadawa mutumin yaje yayi dukkan abinda yake so, shirya nike. Idan Inyamurai suka tambayeni, wani irin bayani zan yi musu.?”

“Ni shugaba ne, dole ne in nemi shawarar kwamitin tafiyar da lamura, gwamnoni, sannan kwamitin zartarwa ta yanke shawara. Kuma kada su manta cewa jam’iyyar nan na da kudin tsari kuma ka’ida shine wajibi a gudanar da zaben fidda gwani ga duk wanda yake son takara.”

Walid Jibrin ya ce tuni ya sanar da jami’an tsaro sun kare shi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Muhammad Isma’il Makama

APC tayi rashin nasara bayan kotu ta tabbatar da Darius Ishiaku na PDP a matsayin halastaccen gwamnan Taraba

Dabo Online

Yan soshiyal midiya ne suka dora Atiku a keken bera – Femi Adesina

Muhammad Isma’il Makama

Da Ɗumi Ɗumi: Jami’an EFCC sun daƙume dan takarar PDP yana tsaka da siyan ƙuri’a

Muhammad Isma’il Makama

2023: PDP ta shiga neman sabon dan takarar shugabancin kasa da zata tisa a gaba

Muhammad Isma’il Makama

Bata gari sun kone ofishin PDP a Kano

Dabo Online
UA-131299779-2