Home LabaraiJihar Kano ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda bayan ritayar Singham

Jihar Kano ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda bayan ritayar Singham

by Dabo Online
0 comments

Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu sabon kwamishinan ta bayan da CP Muhammad Wakili yayi ritaya daga aikin dan sanda bayan cikarshi shekaru 60 a duniya.

Babban siftan ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamau ya bada umarnin nada Ahmed Iliyasu a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kano.

Mai magana da yawun rundunar, DCP Frank Mba ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya fitar a babbar hedikwatar rundunar dake tarayyar Abuja.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00