Hakki ne mu taru wajen Ilimantar da ‘ya yanmu don zama masu daraja in sun girma – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira ga iyaye da su kulawa da ‘yayansu domin sauke nauyin da yake kansu.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a sakon nuna murnar ga ranar da majalissar dinkin duniya ta ware wa yara duniya, “Ranar Yara” “Children’s Day”.

Sakon daya wallafa a shafinshi na twitter, Kwankwaso yace hakki ne daga wuyan iyaye dama al’umma wajen kula da tsare tarbiyya da Ilimin yara.

“Ya rataya a wuyan mu, mu hadu wajen kulawa, Ilimantar da ‘yayanmu domin su tashi cikin bin dokokinmu da al’adu a matsayinsu na manya masu daraja.

%d bloggers like this: