Labarai

An kara wa sojan sama Bashir Umar mukamin da ake shekara 10 kafin a samu

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, NAF, ta karawa jami’inta da ya mayar da naira Miliyan 15 da ya tsinta a Kano zuwa ga mai shi.

Rundunar ta kara masa matsayi zuwa mukamin Kofural, mukamin da ka iya daukarshi har tsawon shekaru 10 bai samu ba.

Ranar 16 ga watan Yulin, Usman Bashir ya mayar da tsabar kudin tarayyar turai na 37,000, kwatankwacin naira miliyan 15 wanda ya tsinta lokacin da yake gudanar da aikinshi a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano dake jihar Kano.

Da yake magana a wajen bikin karrama jami’in da akayi, hafsun hafsoshin sojin sama na Najeriya, Sadiq Abubakar, ya bayyana Usman a matsayin samfurin masu gaskiya.

Inda ya kara da cewa ya nuna cewa ya samu horo mai kyau na iya rikon gaskiya da amana, ya yaba masa tare da cewa rundunar tana mai jinjina masa.

Bayan karin matsayi da Usman ya samu, rundunar ta bashi babbar lambar yabo.

Shima a nashi bangaren, Usman ya nuna godiyarshi da karin matsayin da karramawar da rundunar tayi masa.

Karin Labarai

UA-131299779-2