Home LabaraiAnyi suya an manta da Albasa – Hon Kofa ya tashi a tutar babu

Anyi suya an manta da Albasa – Hon Kofa ya tashi a tutar babu

by Dabo Online
0 comments

A harka irinta siyasa, a iya cewa dan majalissar tarayyar mai wakiltar Bebeji da Kiru, Hon Abdulmuminu Jibrin ya tashi a tutar babu.

Hon Kofa ya kasance jigo a tafiyar tabbatar da Hon Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban majalissar tarayya, hasalima, Hon Kofa ne wanda ya gabatar da Gbajabiamila a matsayin dan takarar shugabancin majalissar tarayya.

Sai dai a wani salo irin na ban mamaki, a ranar 25 ga watan Yuli, shugaban Majalissar, ya nada shuwagabanni a kwamitoci daban daban na kasa da mataimakansu, babu sunan Hon Kofa a cikin jerin sunayen.

Sunayen da suka fito harda ‘ya ‘yan jami’iyyar adawa ta PDP da zasu jagoranci kwamitoci amma babu wanda a iya cewa shine dan gaban goshin kakakin majalissar.

Sai dai masana suna ganin Hon Femi ya kiyaye wa kanshi rikicin da ya faru tsakanin Hon Yakubu Dogara da Hon Kofa, wanda suka samu rikicin tin kafin tafiyarsu tayi nisa.

Rikicin yayi tsamari sosai wanda har ta kai ga an dakatar da Hon Kofa kusan kimanin shekaru 2.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00