//

Da Dumi-Duminsa: Sabuwar Dokar CBN za ta fara aiki a yau Laraba

0

Daga yau Laraba bisa umarnin babban bankin Ƙasa wato CBN, bankunan kasuwanci irin su First Bank da GTBank da Zanith Bank da makamantansu za su fara cazar kwastomomin su adadin wani kaso daga cikin kuɗin da za su ajiye ko kuma za su fitar daga asusunsu, matuƙar dai wannan kuɗi ya kai N500,000 (dubu 500) ga kwastoma ɗaya, ko kuma N3,000,000 (miliyan 3) ga kamfanunnuka da manyan ma’aikatu.
Yadda tsarin yake, idan kaje da niyyar saka N500,000 a cikin asusun ka dole ne bankin zai cajeka kaso 3 na adadin wannan kuɗin, wanda wannan kaso ukun shi ne ya kama N15,000 (dubu 15). Kenan maimakon a baka N500,000 idan kazo cira, sai dai a baka N485,000. Amma idan kana da ragowar kuɗi a asusun sai a cira a cikin su a baka kuɗinka cikakke. Idan kuma ya kasance sanyawa kazo yi a cikin asusun ka bankin zai cajeka kaso 2 na wannan kuɗin, wanda ya kama N10,000. Kenan anan ma ba N500,000 za a sanya maka ba, N490,000 za a sanya maka.
Ga kamfanunnuka da manyan ma’aikatu kuwa, a duk N3,000,000 (miliyan 3) da za su sanya a asusun su banki zai ciri kaso 5, wanda ya kama N150,000 (dubu 100 da 50). Idan kuma cirewa za suyi, bankin zai ciri kaso 3, wanda shi ma ya kama N90,000 (dubu 90).
Kuma wannan dokar za ta fara ne a Jahohi 6 kawai, kafin daga bisani zuwa watan Maris ɗin shekarar 2020 tsarin ya karaɗe dukkan jahohin Ƙasar.
Jahohin sune; Lagos da Ogun da Kano da Abia da Anambra da kuma Rivers.
Dan haka a shawarce, ga wanda ba ya son a taɓa masa kuɗi yana iya raba kuɗin gida biyu, in yaso yau ya kai rabi, gobe sai ya kai rabin. Haka ma kuma in karɓa zai yi, sai ya raba karɓar gida biyu.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020