Labarai

An kori Sarki mai Murabus zuwa jihar Nassarawa – Gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta hannun kwamishinan yada labarai, Mallam Muhammad Garba ta bayar da sanarwar korar Sarkin Kano mai murabus zuwa jihar Nassarawa.

A yau litinin ne dai gwamnatin jihar ta Kano karkashin gwamnan Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta tsige Sarkin wanda ya shafe shekaru 5-6 yana mulkin jihar Kano.

Bayan sanarwar tsige Sarki mai murabus, jami’an tsaro bisa jagorancin kwamishinan yan sandan jihar suka isa fadar masarautar suka hana shiga da fita kafin daga bisani suka fito da Sarki mai murabus daga fadar.

UA-131299779-2