Yanzu- Yanzu: Masu zaben Sarki sun zauna don fidda sabon Sarkin Kano

Karatun minti 1

Awannai kadan bayan da gwamnatin jihar Kano karkashin gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta tsige daga kan mulkin Kano, masu nadin sarkin a Kano sun zauna domin fitar da sabon Sarki.

DABO FM ta tabbatar da cewar yanzu haka masu zaben Sarkin suna zaune a fadar gwamnatin jihar Kano domin fidda wanda zai maye gurbin Sarkin Kano murabus, Mallam Muhammadu Sunusi na 2.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin sun shaida cewa tini dai aka fidda sunayen wadanda za’a iya zaba domin darewa mulkin na Kano ta Dabo.

Majiyoyin sun bayyana sunayen Abdullahi Abbas, shugaban APC na Kano, da ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero guda 2 wadanda suka hada da, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Alhaji Aminu Ado Bayero da Abbas Sunusi Bayero.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog