Hanyar Kano zuwa Kaduna ta zama tarkon mutuwa, bayan da hanyar ta rufta

Karatun minti 1

Matafiya na tafiya cikin dar-dar tare da cunkoso saboda ratse wa gadar Rigachikum bayan ruftawar gadar dake kan hanyar Kano zuwa Kaduna.

Rahoton Dabo FM ya bayyana gadar ta Rugachikum wadda ke a karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna ta rufta ne a ranar Lahadi.

Matafiya sun bayyana mana cewa suna yin zagaye ne domin ratse wa wannan gada wadda zuwa kowanne lokaci zata iya yin kasa baki daya.

Duk wani kokari da hukumar yada labarai ta kasa, NAN tayi domin tuntubar shugaban kula da bangaren na ma’aikatar aikace-aikace ta kasa tayi yaci tura, inda ya bayyana baya gari.

Daga bisani an tuntubi shugaban hukumar kiyaye da hadurra ta kasa (FRSC), Hafiz Mohammed inda ya bayyana mana tini sun tura kwararrun ma’aikatan su domin kula da wannan hanya.

Hafiz Mohammed ya kuma yi kira da matafi su basu hadin kai kana su ringa tuki cikin nutsuwa da kulawa domin kaucewa afkuwar hadurra a kan titin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog