Kiwon Lafiya Labarai

An samu maganin Kwabid-19 a Indiya, ya warkar da mutum sama da…

Jaipur , India (DABO FM) – Kamfanin maganin gargajiya na Pantanjali na kasar Indiya ya kaddamar da maganin Koronabairas mai sunan ‘Coronil and Swasari’.

A taron manema labarai da kamfanin ya kiraa da safiyar yau Talata a shedikwatar cibiyar Patanjali Yogpeeth, ya yi ikirarin maganin ya yi maganin cutar Kwabid-19 dari bisa dari yayin da aka gwada a jikin masu dauke da cutar Kwabid-19.

DABO FM ta tattara cewar kamfanin ya gano maganin ne tare da hadin gwiwar sashin binciken magunguna na Jami’ar NIMS dake garin Jaipur na kasar Indiya.

Da yake bayani a wajen kaddamar da maganin, shugaban kamfanin Patanjali, Baba Ramdev, ya ce maganin ya wuce dukkanin gwaje-gwajen da ya kamata ayi masa.

Hoton wani daga cikin maganin. Hoton Achary Balkrishna

“Kasar nan da duniya baki daya suna jiran maganin cutar Kwabid-19. Muna alfahari sanar da maganin gargajiya na farko da ya cika sharudan lafiya tare da samu shaidar aiki wanda aka samu bayan kwarya-kwaryar binciken Cibiyar Bincike ta Patanjali da Jami’ar NIMS.”

“Maganin ya yi aiki dari bisa dari, ya warkar da masu dauke da ciwo a cikin kanaki 3-7.”

“Zamu kaddamar da maganin Kwabid-19 ‘Coronil and Swasari a yau. Mu gudanar da gwaji guda 2, na farko an yi a Delhi, Ahmedabad da sauran garuruwa. A gwajin a gwada mutum 280 da suke dauke da cutar, dukkaninsu sun warke.”

“Bayan wannan mun sake yi masa gwaji da ake yi wa dukkanin magani a ilimance.”

Shugaban kamfanin ya giodewa cibiyar bincike ta jami’ar NIMS da dukkanin likitoci da masana kiwon lafiya da suka bada gudunmawa wajen binciken maganin.

“da taimakon jami’ar NIMS dake Jaipur, mun gudanar da gwaji akan masu cutar 95. Kaso 69 daga cikin dari na masu dauke da cutar sun warke a kwana 3, a cikin kwana 7 sauran dukka sun warke.

Ya kara da cewa sun samu shalewar gwajin maganin daga dukkanin hukumomin da suke da alhaki bayar da lamunin gwajin magani a kasar Indiya.

DABO FM ta tattara cewar jami’ar NIMS dake Jaipur ta yaye daliban Najeriya sama da 3500 daga shekarar 2010 zuwa 2020, wanda a yanzu take da ‘yan Najeriya sama da 350 dake karatu.

Karin Labarai

UA-131299779-2