/

Jihar Kaduna ta mayar da Almajirai sama da dubu 35 zuwa jihohi 17 – Gwamnati

Karatun minti 1
Nasiru El-Rufai
Mallam Nasiru El-Rufai. Gwamnan Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta mayar da almajirai sama da dubu 35 zuwa Jihohi 17 da ma wanda suka zo daga kasashe makofta.

Kwamishiniyar kula da harkokin Mata da walwalar Jama’a, Hajiya Hafsat Baba ce ta bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a Kaduna, ta ce, zuwa yanzu ita ma jihar Kaduna, ta karbi Almajirai sama da dubu 10 da aka dawo mata da su daga wasu jihohi.

Ta bayyana cewar, matakin na cikin tsare-tsaren da gwamantin jihar ta dauka ne domin samar da tsari mai kyau ga kananan yara bangaren koyon Al-qur’ani da Ilimin Zamani karkashin kulawar iyaye.

Ta kara da cewa, da hadin gwiwar asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya, ma’aikatarta, ta samar da wani tsari na tara bayanai da samar da tsari mai kyau domin bayar da kulawa ta musamman ga Almajiranci da aka dawo da su daga wasu Jihohin kasar nan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog