An sassauta wa masu biyan haraji ne saboda halin matsi-Zaid Abubakar

dakikun karantawa

A kokarin ta na saukakawa al’ummar Jihar Kaduna saboda cutar Covid-19, Gwamnatin Jihar ta sanar da sassauci akan wuraren da suke biyan kudin shiga ga gwamnatin Jiha.

Sanarwar hakan ta fito ne daga shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta Jihar Kaduna Dakta Zaid Abubakar.

Ya ce, tun da duniya ta tsinci kan ta a halin kulle, hukumar sa ta rubutawa gwamnatin Jihar Kaduna rokon a sassauta wa masu biyan haraji ganin an dauki tsawon lokaci kasuwanni da wuraren harkokin yau da kullum na rufe. Kuma gwamnati ta aminci har ta tura wannan bukata ga majalisa, bayan majalisar ta amince ne sai aka fitar da sanarwa ta musamman da take dauke da bayanan sassuacin.

Sanarwar ta kumshi jinkirata gabatar da bayanan haraji daga kamfanoni ko yan kasuwa ko kuma hukumomin gwamnati, Wanda yanzu aka kara wa’adi zuwa 30 ga watan Satumba.
Sai kuma an samar da sassauci na musamman ga duk wanda ya kokarta ya biya haraji a irin wannan lokaci, a inda za’a mayar masa da kashi 1 bisa 100 na abun da ya bayar.
Wannan sassaucin ya shafi gidajen abinci ne da otel da kuma wuraren taruwan Jama’a. su kuma aka dauke masu biyan haraji daga watan Afrilu zuwa watan Satumba su ma.
Sannan Kuma makarantu masu zaman kan su an dauke masu biyan harajin ma’aikatan su a tsawon wannan lokaci. Amma duk wani haraji da ba wannan ba za su biya.

Sannan kuma a kan harajin Kirdado ga kananan yan kasuwa, wannnan kudirin ya nuna cewar an dauke masu biyan harajin har zuwa karshen watan satumba.

A cewar Dakta Zaid Abubakar, hakan na da nufin kara baiwa bangaren kasuwanci dama ne ya kara farfadowa daga halin da ya shiga saboda cutar Covid-19.

Kuma duk wanda ya jima bai biya kudaden haraji ba, wannan kudiri ya bashi daman ya zo domin ya gyara takardun harajin shi, a yi masa sauki domin ya biya abun da ya kamata ya biya cikin sauki.

Ya kara tabbatar da kudirin hukumar sa na inganta bangare biyan haraji a Jihar Kaduna.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog