Kungiyar ‘Ina Mafita Al’umma’ ta yi shagalin Sallah tare da marayu, ta yanka musu raguna 250

dakikun karantawa

Kungiyar Ina mafita Al-umm da ke Zariya Jihar kaduna, ta yi wa marayu 250 layya, tare da baiwa wasu iyayen marayun mata tallafin kudi N10,000  saboda su yi sana’a don samun abin dogaro da kai.

Shugaban kungiyar ta shiyya ta daya a Jihar Kaduna, Malam Bashir Abubakar Magaji, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na hudu da suke wa marayu layya a karkashin kungiyar, baya ga dinka masu kayan sallah da kungiyar ke yi a kowace karamar sallah.

Bashir Abubakar ya ce, daga cikin marayun maza da mata a yanzu haka ana koya ma wasu sana’o’i domin dogaro da kai.

Ya kara da cewa, a shirye suke su cigaba da taimakawa marayu ta hanyoyi daban-daban kamar karatunsu da koya masu sana’a da yin masu sutura da kuma dukkan abubuwa na more rayuwa.

Shugaban ya kuma gode wa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da majalisarsa, da kuma Dan Isan zazzau Alh. Umar Shehu Idris, na tallafawa marayun wannan kungiyar, inda yayi addu’a ta musamman gare su.

Sannan Kuma ya yi Kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa marayun wannan kungiya da iyayen marayun ta hanyar ba su jari domin samun abin dogaro da kai,
ya kuma gode wa sauran shuwagabannin kungiyar na kokarin da suke yi domin ganin ana cigaba da samun kulawa da marayun.

Iyayen marayun da su kan su marayun, sun godewa kungiyar na irin hobasa da sukeyi domin sasu cikin farin ciki.

A karshe, ya ce idan Allah ya kai mu badi su na saran tufatarwa da ciyar da marayu 400, tare da ba iyayen su mata jari Kamar yadda su ka fara.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog