Kaduna: Tsaffin daliban ajin karatu na 2011 a kwalejin Alhudahuda sun gudanar da taro

dakikun karantawa

A Litinin din da ta gabata ne, tsaffin daliban ajin karatu na 2011 na kwalejin Alhudahuda da ke Zariya suka gudanar da gagarumin taro domin gudanar da jawabai da kaddamar da sabbin jagororin da aka zaba da za su jagoranci tafiyar a wannan karo.

Taron da aka gudanar da shi bisa jagorancin tsohon shugaban makarantar Alhaji Muhammad Abbas Aliyu, ya sami halartan mutane da dama musamman tsaffin daliban kwalejin.

Da yake jawabin bude taron, tsohon shugaban kwalejin Alhaji Muhammad Abbas Aliyu, ya tuna irin gwagwarmayar da aka yi fama da shi lokacin da yake jagoranci a makarantar, wanda kuma ya nuna farin cikin sa ganin cewa kokarin da aka yi bai tafi haka kawai ba, saboda sai yanzu dalibai da dama ke ganin amfanin takura da matsawan da aka yi masu a wancan lokaci.

Ya kuma  da cewa, kwalejin Alhudahuda ta zama gagara tsara tsakanin takwarorin ta da suka faro, tunda ta yaye mutane da dama da yanzu Najeriya ke alfahari da su.

Ya nuna muhinmancin samar da kungiya irin wannan, da nufin tunawa da wasu ko taimakon kai da kai. Kuma ya bukace jagororin kada su yi Kasa a gwiwa akan aikin da suka faro na Alheri.

A nashi jawabin, Sabon shugaban Kungiyar tsaffin daliban na ajin karatu na 2011 Malam Nuhu Umar, Ya ce ranar irin ta 2 ga watan ogusta ta zama mai matukar tarihi ga tsaffin daliban za su jima ba su manta da shi ba, kasancewar wasu ma shi ne karo na farko da suke halartan irin wannan taro mai matukar muhinmanci.

Ya kara da cewa, suna cigaba da kokarin shiga lungu da sako domin zakulo tsaffin daliba shekarar ta su saboda su kwadaitar da su muhinmancin wannan tafiya, domin su zo a hada karfi da karfe ko a kai ga gaci.

Ya kara tabbatar da kudirin sa da sauran wanda aka zaba na tafiya kafada da kafada da sauran membobi domin cika dukkanin manufofin samar da wannan tafiya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog