An yanke wa wani malamin jami’an da ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW a shafinsa na sada zumunta hukuncin kisa.
Malamain jami’ar mai suna Junaid Hafeez, yana tsare ne a hannun hukuma bayan ya wallafa kalaman cin mutunci ga Manzon Allah a kafafen sada zumunta a 2013.
Dabo FM ta tattara cewa, hukumomin kasar Pakistan ba sa wasa da duk abin da ya shafi batanci ga addini. Zargin yin batanci ga addini kan jefa wadanda ake tuhuma cikin hadari a kasar, kamar yacce BBC ta tabbatar.
A 2014 ne aka harbe lauyan da ke kare Junaid wato Rashid Rehman, bayan ya amince ya kare wanda ake zargin.
Junaid ya shafe shekaru a killace shi kadai a gidan yarin da ake tsare da shi bayan karuwar farmakin da wasu fursunoni ke kai masa.
Lauyan da ke kare Junaid a yanzu Asad Jamal ya ce hukuncin da kotun ta yanke abin takaici ne kuma za su daukaka kara.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty ta yi zargin rashin adalci a hukuncin, wanda ta bayyana a matsayin “mai ban mamaki da ban takaici”.
