Labarai

Kwashina a Zamfara ya ajiye mukami saboda Matawalle yaki bashi na Kananan Hukumomi

Bayan rahotanni da suka fita a farko na ajiye aikin Kwamishinan Ilimin na jihar Zamfara, Jamilu Zanna, bisa dalilinshi na cewa gwamnan baya kulawa da sha’aninsu, inda ya bayyana har ya gama jinya a kasar Indiya na kwanaki 40, gwamnan bai taba kiranshi yayi masa ko ya jiki ba.

Sai dai majiyoyi daga fadar gwamnatin sun bayyanawa Daily Nigerian cewar ya ajiye aikin Kwamishinan bisa dalilin rashin sakar mara da ya samu daga wajen gwamna Matawalle.

Majiyar ta kara bayyanawa Daily Nigerian cewar Jamilu Zanna, ya so gwamna Matawalle ya barshi yayi rawar gaban hantsi wajen yin mukamai a gwamnatin.

A dai yau Asabar ne tsohon kwamishinan ya kira taron manema labarai a gidanshi dake Gusau, ya bayyana ajiyewar aikin kwamishinan Ilimi.

Karin Labarai

UA-131299779-2