Wasanni

Salah ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar kofin duniya na ajin kungiyoyi

Dan wasan gaba na kungiyar Liverpool kuma dan kasar Misira, Muhammad Salah, ya samu nasarar lashe kambu na gwarzon dan wasa a gasar cin kofin duniya ajin kungiyoyi.

Hakan na zuwa ne bayan nasarar da kungiyar Liverpool ta samu na doke takwararta ta Flamengo dake kasar Brazil.

Kofin duniyar wanda aka buga a kasar Qatar ya samu wakilcin zakarun nahiyoyin da suke dubiya baki daya.

A inda Liverpool ce ta wakilci nahiyar Turai, Flamengo da wakilcin nahiyar Kudancin nahiyar Amerika, Al-Hilal daga nahiyar Asia.

Kungiyar kwallon kafa ta Espérance de Tunis ta fito daga nahiyar Afirika yayin da Kungiyar Monterrey ta fito daga nahiyar Amerika ta tsakiya sai kuma Hienghène Sport daga nahiyar Oceanic da kuma mai masaukin baki kungiyar Al-Sadd ta kasar Qatar.

UA-131299779-2