//

Burin mu shi ne samar da kwararrun dalibai a bangaren aikin Gona – Farfesa Musa Mahadi

dakikun karantawa

Kwalejin horas da aikin Noma da ke karkashin Jami’ar Ahmdu Bello Zariya, ta shirya domin cigaba da bunkasa a bangaren aikin Gona da samar da kwarewa ga dalibai da suke karatu a fannoni daban-daban da suka shafi aikin.

Daraktan kwalejin Farfesa Musa Abdullahi Mahadi, ya bada tabbacin hakan da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa a kan cigaban da aka samu tun bayan kafa kwalejin shekaru 100 da suka gabata, da kuma yanayin da ya riske ta bayan nada shi matsayin sabon jagoran kwalejin.

Ya ce, an kafa kwalejojin ne tun shekaru kusan dari da suka gabata da manufar samar da ingantaccen horo a bangaren noma da kiwo da kuma sarrafa amfanin da ake samu karkashinsu. Sannan kuma zuwa yanzu kwalejin na da rassu guda 3 a fadin Najeriya, da suka hada da ta Mando Kaduna da ta Kaba a Jihar Kogi da kuma babbar cibiyar rukunin kwalejojin da ke Samaru a karamar hukumar  Zariya.

Ya ce, tun bayan zamanshi sabon jagoran kwalejojin, ya yi kokarin dora wa a kan inda tsaffin daraktocin da suka jagoranci kwalejin suka faro domin cika manufar kafa kwalejojin.

Tun a shekarar 1921 aka fara kirkiro ita kwalejin a yankin Maigana da ke Karamar hukumar Soba, kafin daga bisani aka mayar da kwalejin zuwa Samaru, Zariya. Kwalejin ta diba tare da yaye dalibai masu dumbin yawa da yanzu suka zama kwararru a bangaren aikin Gona.

Kuma ana koyarwa ne a bangaren Diploma Babba da Karama da Certificate a bangaren aikin Gona da kuma sauran su.

Ya kara da cewa, irin kalubalen da  ke fuskantar Najeriya, a gaba ana hasashen harkar Noma za ta taimaka wurin bunkasa cigaban tattalin arzikin Kasa.

Sai dai ya koka kan karancin dalibai da ake samu suna shigowa domin koyon dabarun aikin noma, sai ya kwatanta hakan a matsayin rashin dabara da ba zai kai mu ga tudun mun tsira ba.

Daga nan sai Farfesa Musa Mahadi, ya nemi kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatoci a kowanne mataki su shigo domin bada ta su gudunmuwar ta fuskar bunkasa kwalejin da Jami’ar Ahmdu Bello.

Kuma ya yaba wa sabon shugaban Jami’ar Ahmdu Bello, Farfesa Kabir Bala, bisa ‘kyakkyawar manufarsa’ na bunkasa bangaren aikin Gona da kara samar da hanyoyin dabarun koyar da aikin Gona domin Jami’ar ta cigaba da rike kambun ta na zama ta daya a bangaren koyar da aikin Gona a Jami’o’in Najeriya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog