/

Ana samun koma baya ne a kasar nan saboda rashin ‘yan siyasa masu kishin kasa-Ibrahim Ma’adawa

dakikun karantawa

A yayin da ake cigaba da bayyana ra’ayoyi game da ranar samun ‘yancin kan Najeriya na shekaru 60, wasu yan Najeriya na cigaba da bayyana mabanbanta ra’ayoyin su gane da cigaba ko akasin hada da aka samu cikin waddannan shekaru musamman a fagen cigaban tattalin ariziki da siyasa da kuma zamantakewar Kasar.

Na baya bayan nan shi ne wani shugaban al’umma a Zariya ta Jihar Kaduna Malam Ibrahim Ma’adawa.

Ya ce, abubuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da suka hada da tsaro da tattalin arziki da zamantakewa babu wani abu na a zo a gani da wannan gwamanti ta kawo domin saukakawa yan Najeriya ta wannan fuska, tunda har yanzu talakawa na cikin ukuban yunwa da fatara da kuma talauci.

Ya kara da cewa, ko a siyasance yanayin da ake ciki babu wani canji saboda har yanzu Kasar na tsaye wuri guda ba tare da samun wata gagarumar cigaba ba.

Bngaren Noma kuwa, ya ce shi a ganin sa babu wani tasiri ko cigaba da aka samu a bangren banda bakar wahala da mutane ke sha saboda naiman bashin aikin Gona. Kuma an kasa wadata yan kasa da kayayyakin aikin da suka dace domin habbaka bangaren.

Malam Ibrahim Ma’adawa ya ce, halin da yan kasa ke ciki yanzu ba’a fatan cigaba da dawwama a kai, domin mutane kalilan ne ke cin gajiyar gwamantin da ake kurarin kuma ana yi ne domin al’umma.

Ya dora koma bayan da aka samu a kasar nan ga gwamnati mai ci da kuma ‘yan siyasa marasa kishi da son cigaban kasa.

Malamin addinin, ya tunatar da jagorori su rika tunawa da nauyin al’umma da ya rataya a kan su kuma su sani Allah mai tambayar su ne kan abun da suke aikatawa ranar gobe Alkiyama.

Kuma ya hori al’umma da su koma su rungumi sana’oin dogaro da kai domin tsira da mutunci.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog