/

Ɗaki na mahaifina ke biyo ni cikin dare -Yarinyar da mahaifinta ke lalata da ita

dakikun karantawa

An zargi wani mutum mai suna Badamasi ma’aikaci a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria da lalata da diyarsa da ya haifa. Badamasi mazaunin Anguwar ‘Yar tsamiya hayin Dogo Samarun Zariya Samarun Zariya ne.

Manema labarai sun zanta da yarinyar mai kimanin shekaru 14 da haihuwa inda ta bayyana mana cewa, tun da jimawa mahaifin nata mai suna Badamasi ya rabu da mahaifiyar ta kuma da tana zaune ne wurin mahaifiyarta, sai daga bisani ya dawo da ita wurin shi.

Ta ce, ya kan Shigo dakin da take kwana cikin dare ya cire mata kayan da ke jikinta kuma ya rika tura gabansa cikin gabanta, da zaran ta yi kokarin yin ihu sai ya mare ta kuma ya bata tsoron idan ta fada ma wani abun da ke faruwa zai bata mata rai.

A karo na biyu da ya yi yunkurin shi ne ya kira ta da safe ya zuba mata kunu a kofi kuma ya naimi ta shanye, sai dai taki sha ta baiwa wata yar uwanta ne ta shanye.
Don haka sai ta garzaya ta roki mahaifiyar ta cewa gobe ta aiko gidansu da cewa ana kiran ta za ta raka wata ‘yar uwarta anguwa, don haka idan ta fito za ta zo ta sanar da ita abun da mahaifinta ke mata.

Haka ko aka yi kuma bayan ta isa wurin mahaifiyar ne take sanar da ita abubuwan da mahaifinta yake mata, don haka ta sanar da mijin da take aure yanzu mai suna Isiya Dahiru, suka sanar da wata kungiyar mai rajin kare hakkin Dan Adam Mai suna ‘She Initiative’ a turance, daga nan kuma suka garzaya ofishin ‘yan sanda suka sanar da su halin da ake ciki kuma aka bayar da umarnin damko shi wanda ake zargin mai suna Badamasi.

Nan aka cigaba da bin sauraran bahasi da farko yaki amsa laifinsa sai daga bisani kuma ya amsa.
Sai dai abubuwa da dama sun shigo bayan da aka zargi wannan kungiyar ta ‘She Initiative’ da karkatar da laifin ta hanyar naiman yin sulhu.

Duk da daga bisani manema labarai sun zanta da ita jagoran kungiyar, Malama Talatu Magaji Kuma ta karyata zargin da ake mata na karkatar da laifin, ta ce tana iya bakin kokarin ta don ganin an binciko gaskiyar lamarin kuma an hukumta mai laifi.

Da kuma mai Anguwan Hayin Kwamanda mai suna Malam Muhammad Yakubu, kuma shi dan uwa ne ga wanda ake zargin. Haka kuma ‘yan uwan mahaifiyar yarinyar da abun ya faru sun zarge shi da hada baki da makala masa ciwon hauka na karya domin yin kofar rago a binciken da ake.
Shi kuma manema labarai sun yi kokarin ji ta bakin sa hakan ya ci tura.

Daga bisani an garzaya da mai laifin shelkwatar yan sanda da ke Kaduna domin cigaba da gudanar da bincike.

Kakakin rundunar yan sandar Jihar Kaduna, Muhammad Aliyu Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce za su cigaba da yin duk mai yiwuwa domin gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog