Anyi yunkurin harba makamai masu linzami a birnin Makkah da Jeddah.

Karatun minti 1

Rundunar sojin saman Saudiyya ta ce ta samu nasarar dakile wasu hare-haren makamai masu linzami biyu da ‘yan tawayen Houthi suka yi yunkurin kai wa biranen Makkah da Jeddah ranar Litinin, kamar yadda kafar yada labarai ta Al Arabiya ta ruwaito.


Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa jaridar Al Arabiya ta rawaito cewa rundunar sojin kasar ta Saudiyya ta tarwatsa makaman da kungiyar yan tawayen suka harbo.


Gwamnatin Yemen ta soki harin, inda ya bayyana shi a “mummunan aikin ta’adddanci.”

Tin makon daya gabata ne ‘yan tawaye suka fara shirye-shiryen janyewarsu daga tashar jiragen ruwa ta Hudaydah da sauran makotan yankin a matsayin matakin farko tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tin a watan Disamba.

Gwamnatin Yeman da ‘yan tawayen Houthi sun cimma yarjejeniyar ta barin tashar jiragen ruwan ne domin ssamun damar shigowa da kayayyakin tallafi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog