Labarai Siyasa

APC ta kori Hon Gudaji Kazaure

Jami’iyyar APC ta karamar hukumar Kazaure ta kori Hon Gudaji Muhammad Kazaure daga jami’iyyar.

Hakan na dauke a cikin wata sanarwar da jami’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun dukkanin shuwagabannin jami’iyyar karamar hukumar a ranar 25 ga watan Maris din 2020.

Dan majalisar ya kasance wakilin kananan hukumomin Roni, Gwiwa, ‘Yan Kwashi da Kazaure a majalissar wakilai ta Najeriya.

Sanarwar tace; “Mu shuwagabannin jami’iyyar APC na mazabar Yamma, karamar hukumar Kazaure jihar Jigawa, mun amince da korar Muhammad Gudaji Kazaure daga jami’iyyarmu ta APC daga yau 25 ga Maris 2020.”

Jami’iyyar tace ta kori dan majalissar ne bisa rashin bin dokokin da umarnin jami’iyyar da dan majalissan yake yi.

Shugaban jami’iyya, mataimakinshi, Sakataren jami’iyyar da sauran masu mukami guda 16 na jami’iyyar APC a matakin mazabar Yamma ta karamar hukumar ne suka amince da korar dan majalissan.

Karin Labarai

Masu Alaka

Bana cikin taron hadin kan APC na ‘Babba-da-Jaka’ da Yari ya kira -Sanata Marafa

Muhammad Isma’il Makama

Kotun koli ta kwace zaben dan majalissar tarayya na APC a jihar Adamawa

Dabo Online

Sabon Cajin Banki, fashi da makami ne – Hon Kazaure

Dabo Online

Zaben Gwamnoni: Ku zabi gwamnonin da jam’iyyar APC ta tsayar takara kawai – Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu

APC ta shirya korar Abdul’aziz Yari daga jami’iyyar

Dabo Online

Ban zagi Buhari ba, ban kuma ce ya gaza ba – Hon Gudaji Kazaure

Dabo Online
UA-131299779-2