Arewa 24 ta fara daukar shirin Kwana Casa’in Kashi na 2

Gidan Talabijin na Arewa 24 ya fara daukar cigaban shirin Kwana Casa’in kashi na 2 wanda take gabatarwa a tasharta duk ranakun Lahadi.

Daya daga cikin jarumawan dake taka rawa, a shirin, Abba S Boy ne ya bayyana haka a shafinshi na Facebook a ranar Talata.

Inda aka hangeshi tare da madauka shirin a lokacin da suke daukar sabon shirin.

Arewa24 ta gintse shirin Kwana Casa’in ne bayan ta gabatar da na mako 13, a ranar 1 ga watan Yuli. (Ranar da suke daura a manhajar Youtube na karshe)

Har yanzu ba’a san ranar da shirin zai dawowa makalla shirin ba, sai dai DABO FM ta binciko cewa akwai yiwuwar shirin zai dawo ne a watan Disambar 2019.

%d bloggers like this: