Home LabaraiKwartanci da Munafurci yayi yawa tsakanin Ma’aurata masu amfani da wayar hannu – Daurawa

Kwartanci da Munafurci yayi yawa tsakanin Ma’aurata masu amfani da wayar hannu – Daurawa

by Dabo Online
0 comments
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa a yan kwanakin nan maganar kwartanci da munafurci da boye-boyesunyi yawa tsakanin ma’auratan dake amfani da wayar Hannu.

Duk da dai cewa Sheikh Daurawa yayi wannan furuci ne tin a watan Fabarairun 2019, kamar yacce yake a kwanan watan dake kan rubutun da yayi a shafinshi na Facebook.

DABO FM ta binciko cewa Sheikh Daurawa ya bayyana haka ne a dai dai lokacin da aka samu wata mata da ta kashe Mijinta akan yana waya da wata.

Sheikh yace

“Al’amarin kashe kashe tsakanin ma’aurata, saboda tsakanin kishi da zargin soyayya da wata ko da wani da kuma matsalolin amfani da wayar hannu ya fara yawa
Mai yasa wasu maza suke boyewa matansu wayoyinsu?

“Mai yasa wasu mata suke boyewa mazansu wayoyinsu?

A dan tsakanin nan maganar kwartanci da munafinci da boye boye yayi yawa tsakanin masu amfani da wayar hannu ma’aurata. 

Yaya zamu shawo kan wannan matsala domin ta fara muni sosai. 

Allah ya gyara mana tsakanin mu.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00