Home LabaraiAmurka ta koro ‘yan Najeriya sama da 370 bisa saɓa ƙa’idoji

Amurka ta koro ‘yan Najeriya sama da 370 bisa saɓa ƙa’idoji

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
Amurka ta kori 'yan Najeriya

Gwamnati kasar Amurka ta nemi wasu wasu ‘yan Najeriya sama da 370 da su fice su bar kasar bisa karya wasu dokokin kasar.

Cikin laifukan da gwamnatin kasar ta ce ‘yan Najeriya sun aikata sun hada da karya dokar shige da fice da laifuffukan cuta da ake aikartawa a yanar gizo.

Tini dai wasu kotuna a jihohin Texas, New York da California da wasu jihohin suka tabbatar da ‘yan Najeriyar su 370 da laifuffukan da ake tuhumarsu da su.

Zuwa yanzu, kasar Amurka ta kori ‘yan Najeriya sama da 3000 bayan tabbatar da samunsu da laifi da wasu kotunan kasar suka yi a cikin shekaru 15 da suka gabata, kamar yadda Jaridar Premium Times ta fitar da alkaluma.

Kazalika a cikin shekarar da muke ciki, a cikin watanni shida da suka gabata, an samu ‘yan NAjeriya sama da 335 da suka shiga kasar Amurka ba bisa ka’ida ba yayin da wasu suka shiga da izinin shiga na Visa wanda yake na bogi.

Sai dai duk da haka, ‘yan Najeriya suna daga cikin bakin haure da sukafi na kowacce kasa bai wa kasar Amurka gudunmawar ta fanni daban daban.

Mafi yawan ‘yan Najeriya da suke zaune a kasar suna aiki, tare da cewa akwai Injiniyoyi da Likitoci da yawa a cikinsu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00