Atiku ya bukaci mataimakiyar Buhari ta biyashi miliyan 500 bisa yi masa kazafi

Karatun minti 1

Dan takarar shugaban kasar Najeriya, karkashin jami’iyyar PDP a zaben 2019, ya nemi mataimakiyar shugaba Buhari ta fannin labarai, Lauretta Onochie, ta biya shi naira miliyan 500 bisa abinda ya kira yada karya akan shi (Atiku).

A wata takarda mai dauke da saka hannun lauyan Atiku, Mike Ozekhome (SAN), takardar tace Onochie ta wallafa wani sako ta twitter inda tace “Atiku yana da cikin mutanen da jami’an tsaron kasar UAE suke sakawa ido.

Atiku yace babu batun cewa jami’an tsaron kasar sun sanya shi a wanda suke sawa ido.

Yace zai kai Onochie kotu, kuma ta biya Naira biliyan 2, idan har bata rubuto masa rubutacciyar takardar neman gafara da kuma biyan miliyan 500 ba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog