Matsalarmu a Yau

Matan Aure sun fara kokawa kan yacce Mazajensu ke aikensu siyo abu a lokacin da suke tare.

A cigaba da kawo muku abubuwan da ke wakana a shafukan sada zumunta musamman a Instagram, yau ma mun sake yin nutso a shafin nan na Northern Blog, shafi dake tattauna batutuwan Matasa da matsaloli na ma’aurata tare da neman shawara ko bukatar a duk sanda hakan ta taso.

Yau ma mun sake zakulo muku wani batu inda wata matar aure ta kawo karar mazaje akan yadda suke wahalar da matansu musamman a ayyuka da suke ba na gida ba, kamar aiken siyo wani abu a lokacin da suke tare ta mijin.

Matar data bukaci a boye sunanta tayi rubutu kamar haka;

“Duk munsan yanda azumin nan ke wahalar da kowa. Jiya munje asibiti yarinyata ba lafiya wajen 5 na yamma, bayan munga Likita, an rubuta mata magani, Mun tsaya a shagon magani zamu siya.
Abin mamaki! Wai sai kawai ya miko min kudin wai in shiga in siyo mata, nace ban gane ba, budan bakinshi wai shima yana fama da ciwon kai, har ulcer shi na son tashi bla bla. Maimakon na tsaya bata lokaci sai kawai na fita na tsallaka titi na siyo. “

Bayan na fito daga shagon maganin din kafin na tsallaka titi wata mota ta tsaya. Abinda ya daure min kai, nan ma matan ta fito ta bar mijin da yaranta ciki, taje wurin masu siyar da kayan marmari da kosai, ta siya. Abin ya bata min rai, wai basa tausayinmu ne?
Aikin gida, ga yara, kuma duk dai mu zamu hada abincin buda baki. A share awanni a cikin Kitchen dan a birgesu amma in kika sake aka kira sallah baki gama hada abincin ba kin shiga uku, ko sau daya ne baza’ayi miki uzuri ba.


Bayan na koma cikin motar, bakina ya kasa yin shiru na fadi mishi. Abinda yafi bata min rai sai cewa yayi, “all what a man can do a woman can do it better” “Duk abinda namiji zan iya, mace ma zata fishi yi da kyau.”, mata sun fi iya cinika idan shi zai siya abu tsada ake yi mishi.


Daman ba yau ya fara ba amma da yau duk yafi bata min rai. Yafi kowa sanin nima ba lafiya gareni ba amma bai tausava min ba.”

Ko mai zaku iya cewa game da wannan batun?

Zaku iya bayyanawa a shafinmu na Facebook, DaboFM

Karin Labarai

Masu Alaka

Hotuna: Daurin auren ‘yar Gwamnan Zamfara da angonta mai shekaru 22 a duniya

Dabo Online

Anyi baikon Yaro dan shekara 17, da Amaryarshi ‘yar 15 a jihar Sokoto

Dangalan Muhammad Aliyu

Wasu Matan Arewa suna nemawa Mahaifiyarsu mai shekaru 60 miji a shafukan sada zumunta

Dabo Online

Ina son mutumin da matar shi ta caccakawa wuka idan zai aureni – Budurwa

Dabo Online

An daga auren Sulaiman da baturiyar Amurka ‘sai baba ta gani’

Dabo Online

Cikin Hotuna: Auren ‘dan shekara 19 da Amaryshi mai shekaru 39

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2