Labarai

Kansila a jihar Nassarawa ya angonce da mata biyu a rana daya

Kansilan mazabar Iwogu, Ibrahim Oboshi, ya auri zankadaddun mata guda biyu a rana guda.

Kansilan ya auri mata biyu wadanda aka bayyana da Nazira Ozegya da Rabi Akose kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Rahotan yace sunayen matan guda biyu da na Kansilan aka buga a jikin katin gayyatar daurin auren da akayi ranar 28 ga watan Maris.

An dai daura auren Ibrahim Oboshi da Nazira Ozegya da misalin karfe 10 na safe ranar 28 ga wata a unguwar Keana.

Yayin da aka daura aure na biyu tsakanin Kansilan da Rabi Akose da misalin karfe 12 a unguwar Obi.

Duk da kasancewar angon a matsayin kansila, ya bayyana cewar shi manomi ne.

Zuwa yanzu dai tini amaren da angon suka tare a gida guda.

Karin Labarai

UA-131299779-2