Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

A kullin muna godewa Allah Mahalicci da yake kara bamu ikon yin tunani mai zurfi don fahimtar al’ummar rayuwa.

Sanin kowa ne, matasa sune kashin bayan cigaban kowacce al’umma, mai yin musu akan haka ya bincike tarihin Sayyadina Ali, Zaidu Bn Haris da Mus’ab Bin Umair, Allah Ya kara yadda a garesu.

A dai dai lokacin da aka mayarda matasan Arewa bayi, wajen daukarsu a matsayin ‘yan bangar siyasa da zama a sahun gaba wajen aikata ta’addanci a tsakanin al’umma.

Sai gashi Allah ya kawo mana dauki mai alkhairi na mutum mai kishin jama’arshi, mai kalamin “Kowa mai daraja ne”, “Kowa zai iya zama tauraro”, “Matasa”, “Ilimi” da “Lafiyar Iyayen mu Mata”

A lokacin shine Talaka ya sauka daga kan wani layi da aka dora mutane na cewa “Masu abu da abunsu”, wato duk wani cigaba yana wajen ‘ya yan masu mulki, kudi da Sarauta.

Allah ne kadai yasan ‘ya yan talakawa ‘yan jihar Kano da suka zama mutane masu daraja a idon duniya ta hanyar morar tallafin Ilimi kyauta da sana’o’in a zamanin wannan bawan Allah. Dalibai sama da 2000 ya tura kasashen waje inda ‘yayan masu hannu da shuni suke tura nasu.

Masu Alaƙa  Alakar dan Majalissar tarayya na Fagge da Al’ummar da yake wakilta, Daga Umar Aliyu Fagge

Tin daga nan ne wasu daga cikin manyan masu mulki da kudi suka fara rigima da Kwankwaso, akan cewa meye zai mayarda ‘ya ‘yan talakawa abinda yasa a gaba?

Haka zalika yanzu ma da gidauniyar daya kafa take neman tallafin kudade don daukar nauyin matasa 370 zuwa kasashen waje don yi Ilimi, suke tada jijiyar wuya suna fadin wai tsohon Sanata ya zama ‘dan 419.

Sauran ‘yan uwanmu matasa masu bin tafiyarsu suna kyamatar abin bawai don basa so ba, sai dan dama sun kashe musu zuciya.

Ya kai matashi, lokacin da ake tattara takardun matasa daga cikin 370 din da za’a fitar yanzu, suka zuga ka don kar ka kai takardun ka saboda basa so ka dena musu bauta.

Masu Alaƙa  Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Yanzu ma ance a tallafa sunce karka bayar wai damfara ce, sun manta da kudaden da kuka tarawa “Yawale ya ware dasu zuwa garin “yan Shey da da ni”, saboda baso su rasa masu musu fadanci.

Wallahi da kanka zaka ciji yatsa, kana zaune kana zagin Kwankwaso wadannan dalibai 370 zasu je su dawo kai kuma kana bakin titi kana zagin Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya.

Da zarar ka girma kuma su koreka, idan ka matsa suyi maka tallan aikin gadi ko ka kare a matsayin dan aiken Hajiyar gida matar Hon.

Ya dai kamata ayi tunani.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Masu Alaƙa  Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: