Labarai

Kayi mini aure ko na shiga duniya – Budurwa zuwa ga Mahaifinta

Shashin Hausa na Legit Ng ya rawaito;

Yanzu wani zamani ne da muke ciki da ba wuya halayen yara ya gurbace, musamman ‘ya’ya mata Akwai babbar matsala ga halayen ‘yan mata wadanda suka nemi iyayensu suyi musu aure suka ki.

‘Yan mata masu yawan gaske suna shiga harkar karuwanci, shaye-shaye, idan har suka bukaci aure iyayensu suka ki yi musu.

A lokuta da dama ‘yan mata na bukatar aure sai iyayensu suki amincewa saboda suna so suyi karatu, ko kuma ta kawo wanda basu so, kuma wani dalili nasu.

Akwai wata yarinya da ta bukaci mahaifinta yayi mata aure, har ta kawo mishi saurayin da take so, amma uban yarinyar yaki yarda, a karshe yarinyar ta rubuta masa wata wasika, inda take cewa: “Na tafi idan ka zo lahira Allah zai yi mana hisabi.” Kawai sai ta hau saman bene ta fado ta mutu a take a gurin.

Haka ita ma wata budurwa ta samu mahaifinta akan tana son yayi mata aure ko kuma ta shiga duniya.

Iyaye na da babban kalubale a gaban su, idan aka yi la’akari da irin abubuwan da ke faruwa a wannan lokacin, akan yadda yara ke lalacewa, da kuma wannan sabon bala’in da ya fito na yanzu, wanda haka kawai za a iske mutum ya kashe kanshi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hotuna: Daurin auren ‘yar Gwamnan Zamfara da angonta mai shekaru 22 a duniya

Dabo Online

Ina son mutumin da matar shi ta caccakawa wuka idan zai aureni – Budurwa

Dabo Online

Anyi baikon Yaro dan shekara 17, da Amaryarshi ‘yar 15 a jihar Sokoto

Dangalan Muhammad Aliyu

Ango Abba da amaryarshi sunyi watanni 2 da aure

Dabo Online

Matan Aure sun fara kokawa kan yacce Mazajensu ke aikensu siyo abu a lokacin da suke tare.

Dabo Online

Hotunan Daurin Auren Abba, angon shekara 17 “Angon Shekara”

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2