Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Diclofenac yana kara janyo afkuwar ‘Bugawar Zuciya’ da kaso 50

2 min read

Likitoci a kasar Indiya, sun gudanar da bincike akan kwayar Diclofenac wanda ya hada da su Ibprofen da sauran kwayoyin na dangin NSAIDs.

Likitoci sunce dangogin magungunan NSAID, sune magungunan da aka fi amfani dasu a fadin duniya, saboda karfin su na rage radadin ciwo. Daga cikin magungunan dangin NSAIDs, sun hadar da Diclofenac, Aspirin, Indocin, Ibuprofen da sauransu.

“Diclofenac is a non-steroidal drug used for alleviating pain in patients suffering from gout, but it is also been found to increase the risk of heart attacks and stroke by 50%, according to a recent research where more than 6.3 million cases were studied.”

“Diclofenac nau’in magani ne dake warkar da radadi da zafin ciwo ga masu lalurar ‘Gout’, ciwon dake shafar gabbai da sauran sassa. Sai dai bincike na nuna yana taimakawa wajen kara afkuwar bugawar zuciya da kaso 50.

“Binciken ya ce anyi binciken ne a sama da marasa lafiya miliyan 6 da dugo 3 (6.3).”

Likitocin sun kara da cewa, Diclofenac din yafi sauran magungunan NSAIDs karfi wanda hakan yasa yana kuma kara bada damar zub da jini a cikin ciki “Gastrointestinal Bleeding.”

Diclofenac yana iya haifar da jerin wadannan cututtuka kamar haka;

  • Amai da Gudawa.
  • Tashin Zuciya
  • Ciwon Kai
  • Yana kawo raguwar cin abinci.
  • Jin jiri
  • Shiga cikin damuwa.

Idan har aka dirfafi shan shi babu kakkautawa, yana kawo illa ga jerin wadannan;

  • Ciwon Hanta
  • Ciwon Koda
  • Ciwon Zuciya
  • Ulcer

Yana janyo rashin warkewa da wuri idan anji ciwo da kuma kashe sinadarin da yake taimakawa wajen tsayar da jini yayin ciwo.

Daga karshe anyi kira ga likitoci dasu rika binciken mara lafiya sosai kafin rubuta masa wannan magani.

Idan an samu mara lafiyar da maganin bai karbe shi ba, yana da kyau a chanza shi, ko kuma wadanda suke da Ulcer da sauran cututtukan da aka lissafo.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.