Labarai

Babu ta yadda za’a iya yakar rashawa bayan akwai tsare-tsaren dake taimakawa wajen karuwar talauci -Falana

Babban lauya a Najeriya,S AN Femi Falana ya bayyana babu ta inda za’a kawo karshen cin hanci da rashawa bayan gwamnati tana fito da sabbin tsare-tsaren dake habaka fatara da talauci a Najeriya.

Majiyar Dabo FM ta jiyi gogaggen lauyen na fadin haka inda ya kara da cewa shugabannin Afirka sun kasa fitowa su fadi gaskiyar abinda ke kawo rashawa a yankin.

Lauyan ya fadi hakan ne a wani taron kawo karshen cin hanci da rashawa kashi na 8 da akayi a ranar Laraba a babban birnin tarayya dake Abuja.

Daga karshe yayi kira da shugabanni musamman na Najeriya dasu fito da hanyiyin da zasu rage fatara da talauci tanan zasu sanu nasarar yaki da cin hancin da suke ikirarin suna yi.

UA-131299779-2