//
Wednesday, April 1

Kungiyar mata ‘yan asalin jihar Jigawa sun fara aikin bada magani kyauta a fadin jihar

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar mata ‘yan asalin jihar Jigawa mazauna garin Kaduna tana kan duba marasa lafiya kyauta a jihar.

Kungiyar mai suna ‘Better Life for Jigawa Women wacce take karkashin jagorancin Umma Muhammad, yar asalin gundumar Bamaina dake karamar hyukumar Birnin-kudu.

Kungiyar wacce take da Shedukwata a garin Kaduna, tana gudanar da harkokin lafiya ne ga mata da masa yara da manya kyauta, musamman masu cututtukan Idanu, Sikila, Olsa da kuma duk wata lalura dake jikin Dan Adam.

A zantawar wakilinmu na jihar Jigawa Rilwanu Labashu Yayari da shugabar kungiyar, ta shaida cewa, suna gudanar da ayyukansu ne domin jinkai.

Shugabar kungiyar Hajiya Umma Muhammad, ta kara da cewa a duk rana a kalla suna yi wa mutane 300 ko sama da haka aiki. Ta kara da cewar suna duba sassan jikin mutum ne ta hanyar amfani da na’ura bincike kafin bayar da magani.

Masu Alaƙa  Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisa a Jigawa

Umma Muhammad tace, suna samun kudaden shiga ne ta hanyar taimakon wasu bayin Allah da suka hadar da, Farfesa Usman na Jami’ar Abuja, Abdullahi M Nasiru shugaban Mamiya Oil, Alhaji, Abdullahi Uba Zaria da kuma ita kanta Umma Muhammad wacce take harkokin kasuwanci a Kaduna.

Wakilin mu ya ganewa idonsa yadda wannan kungiya ke gudanar da ayyukanta, da kuma yadda mutane suke gamsuwa da ayyukan kungiyar.

Kungiyar tasha alwashin ziyartar kowacce karamar hukuma a fadin jihar Jigawa, wadda yanzu haka take kan karamar hukuma ta Biyar cikin Ashirin da Bakwai na jihar Jigawa.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020