Labarai

Ya kamata ‘yan jaridu su yi amfani da aikin su wurin kare martabar kasar nan-Manjo Janar Sani Muhammad

An bukaci manema labarai su yi amfani da aikin su wurin kare martabar kasar nan da mutunta ayyukan hukumomin tsaro masamman na soji domin tabbatar da kasar nan ta zauna lafiya cikin lumana.

Shugaban makarantar horas da kwaratan soji da ke Zariya wato Nigerian Depot Army Zaria Manjo Janar Sani Muhammad, ya bayyana hakan sa’ilin da ya karbi bakuncin shuwagabannin kungiyar ‘yan jaridu ta kasa shiyyar Zariya a ofishin sa.

Ya ce, bukatar manema labarai su kare daraja da martabar kasar nan ya zama dole, saboda yadda tabarbarewar tsaro ta addabi wasu sassan kasar nan.

Ya kara da cewa, kokarin da ‘yan jaridu ke yi a koda yaushe abun a yaba ne, ta yadda sukan zama tsani tsakanin hukumomi da wanda ake jagoranci musamman a yankunan karkara.

Manjo Janar Muhammad, ya kwatanta dangantaka tsakanin sojoji da ‘yan jaridu a matsayin dadaddiyar dangantaka, wanda ya yi fatan za ta daure har illa ma sha’ Allah.

Ya gode ma membobin kungiyar ‘yan jaridun saboda ziyarar da suka kaiwa makarantar horas da kwaratan sojin da ke Zariya, sannan ya tabbatar da kudirin makarantar na cigaba da gayyatar manema labarai a lokuta daban-daban musamman lokutan da suke gudanar da wasu tarukan su.

Da yake maida jawabi, shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa shiyyar Zariya Kwamared Bello Habib, ya gode ma kwamandar bisa amsar tawagar da ya yi da kuma karrama su. Sannan ya bayyana kudirin membobin kungiyar na kyautata dangantaka tsakanin ta da rundunonin tsaro da ke shiyyar Zariya domin kawar da matsalar tsaro a yankunan karkara da birane.

Karin Labarai

UA-131299779-2