Labarai

Babu wani rikicin a masarautar Kano, sabbin masarautun kuma nanan daram – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta karyata labarin dake bayyana akwai wani rikici tsakanin ta da masarautar Kano akan nadin sabbin sarakuna.

Majiyar DABO FM ta tuntubi mataimakin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta bangaren kafafan sadarwa, Abubakar Aminu Ibrahim don jin ta bakin Gwamnatin, inda ya bayyana wannan labarin kanzon kurege ne.

Ya kuma kara da cewa siyasa ce Wanda Yan kwankwasiyya suke so su tada rikici a jihar ta Kano.

UA-131299779-2