0
Gwamnatin tarayya ta rage kudin man fetur daga N145 zuwa N130 kowacce lita daya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ragin yayin gudanar da zaman Majalissar Zartawa wanda aka gudanar a yau Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan da farashin gangar mai a kasuwar duniya ya fadi warwas wanda karyewar na da alaka da barkewar cutar Corona Virus.
