Labarai

NYSC ta dakatar da sansanonin bautar kasa

Hukumar dake kula da alhakin shirin Bautar kasa ta Najeriya ta dakatar da jami’an dake cikin sansani da kuma wadanda ke kokarin shiga Sansanin.

Sansanin wanda aka bude shi ranar Talata, an bada umarnin rufe shi yau sakamakon samun mai dauke da cutar Mashako (coronavirus) mutum na Uku a Najeriya.

Hukumar ta tabbatar da wannan mataki ne a shafinta na Facebook.

Hukumar ta tabbatar wa da jami’an dake sansani cewa, Yanzu za a tura su zuwa wuraren aikin su kai tsaye.

Sanarwar tace biyo bayan katse shirye-shiryen wasannin kasa sakamakon cutar coronavisu, itama wannan hukuma tana mai sanar da kashe harkoki a cikin sansaninta.

Don haka ake sanar da jami’an cewa, Yanzu za su wuce wuraren aikin su, zuwa lokaci da komai zai daidaita kafin nan su dawo sansanin, Kamar yadda ya faru a baya lokacin cutar Ebola.

Masu Alaka

EFCC ta fara farautar ‘Yan Najeriya dake shiga NYSC da kwalin bogi musamman dan Kwatano

Dabo Online

Katsina: Matasa 3 dake yiwa kasa hiduma a NYSC sun rasa Rayukansu a hatsarin Mota

Dabo Online
UA-131299779-2