Ban gina sabbin gidaje ko siyan hannayen jarin gida ko kasar waje ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dukkanin dukiyar da ya mallaka a shirin rantsar dashi wa’adin mulkin Najeriya karo na byu kamar yacce doka ta tanada.

Za dai a rantsar da shugaban ne karo na biyu a yau Laraba0, 29 ga watan MAyu bisa tsarin doka.

“SHugaban yamika takardar bayanan dukiyoyin daya mallaka ne ta hannun mataimakin shugaban a fannin harkokin cikin gidan shugaban kasa, Sarki Abba, a daren jiya” kamar yadda Mallam GArba Shehu ya bayyana a wata takarda mai dauke da sa hannunshi.

DaboFM ta rawaito Fadar Gwamnatin tace “Takardun bayanan da shugaba Buhari ya sanyawa hannu, ya kuma rantse akan gaskiyarta, ba tada banbancin da irin wacce ya mikawa hukumar a shekaru 4 da suka gabata.

“Babu sabbin gidaje, babu sabon asusun bankin cikin gida ko na kasar waje kuma babu sabbin hannayen jari.

DaboFM ta binciko cewa shugaba Buhari ya bayyana kadarorin da ya mallaka a shekarar 2015 tin kafin a rantsar dashi.

Daga cikin kadarorin daya mallaka; Buhari yace yana da naira miliyan 30 a asusun bankinshi.

Shanu 270, Raguna 25, Dawakai 5, tsuntsaye , gidaje 5 a jihohin Kaduna, Dura, Kano, da Abuja wanda ya bayyana gidan Daura na kasa ne.

Yana da filaye a Portharcourt da Kano tare da wasu motoci.

Shugaba Buhari yanada asusun a bankin Union, yace bashida asusun kasar waje ko ma’akata.

%d bloggers like this: