(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Akwai yiwuwar sake komawa wa’adina na biyu da wasu tsofaffin Ministocina – Buhari

Karatun minti 1

Shugaba Muhammadu Buhari yace Akwai yiwuwar ci gaba da aiki da wasu daga cikin tsaffin Ministocinshi a zangon “Next Level”.

Buhari ya baiwa Ministocin umarnin rubuto sakamakon ayyukan da suka gudanar da nasarori a baya, tare da umarnin mika takardun bakwana da aikin ga sakatarorin ma’aikatunsu.

Cikin wata ganawa da yayi da gidan Talabijin na NTA, Buhari ya shaida cewa lallai ne kowa ya tashi tsaye musamman fannin sha’anin tsaro da sharia.

Ya tabbatar da hukunta duk wanda aka kama da laifin yin wasa da aikinshi musamman a bangaren sha’anin tsaro da Shari’a

Sashin Hausa na Jaridar Leadership ya rawaito “Ya ce (Buhari) duk wanda aka samu yana wa ayyukan wadannan fanni zagon kasa zai kuka da kan sa.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog