Ban taba zaton akwai takin zamani kamar na NARICT ba-Sarkin Noman Makarfi

dakikun karantawa

An yi kira ga gwamnatoci a kowanne mataki da kungiyoyi masu zaman kan su da kuma kamfanonin gudanar da aikin gona su rika amfani da takin zamani da ake sarrafawa a Cibiyar binciken sinadarai ta kasa da ke Zariya, wato National research institute of chemical technology NARICT, a turance.

Kiran ya fito ne daga Sarkin Noman Makarfi Alhaji Danladi Mai Kwai sa’ilin da ya kai ziyara Cibiyar domin duba yadda ake sarrafa albarkatun da ke cikin al’umma ana maida shi takin zamani.

Ya nuna matukar farin cikin sa bisa abin da ya gani ana sarrafawa a Cibiyar, wanda ya ce shi a tsawon rayuwar sa bai taba zaton akwai cibiya a kasar nan da ta ke da ilimin sarrafa albarkatun kasa kamar ‘ya’yan Dalbejiya da K’aro da Kashin kaji da kuma Kasa domin samar da ingantaccen taki da yakan fi shekara yana aiki a kasa ba.

Ya bayyana hakan a matsayin cigaban da ya kamata a ce dukkanin gwamnoni 19 na Arewacin Najeriya da ‘yan majalisu da ma kamfanoni sun zo sun yi wani hadin gwiwa na musamman da Cibiyar ta NARICT domin kara habbaka takin da ake sarrafawa a cikin ta.
Inda ya ce, matukar aka samu irin wannan hadin gwiwa zai taimaka wurin rage koke-koken da ake na rashin wadataccen takin zamani mai inganci a kasuwanni.
Kuma ya kara ma abun da ake nomawa kyau da ingancin da zai kara daraja a kasuwanni.

Sarkin Noman Makarfi ya gode ma hukumar gudanar Cibiyar binciken ta NARICT bisa jagorancin Farfesa Joeffry Barminas da kuma daraktan tsare-tsare da gudanarwa Malam Rabi’u Haladu bisa tarbar da suka yi masu, sannan suka yi fatan kara samun jagoranci na gari kuma abun koyi ga yan baya.

Da yake maida jawabi, shugaban Cibiyar binciken sinadarai ta kasa da ke Zariya Farfesa Joeffry Barminas ya ce, kokarin da suke domin sarrafa albarkatun kasa na taimawa wurin rage yawan kayyakin da ake shigowa da su kasar nan, da ya ce Najeriya tana asarar miliyoyin daloli duk shekara saboda shigowa da wasu kayayyakin daga kasashen ketare.
Kuma ya ce ko a makon da ya gabata ma ya gayawa kwamitin kimiyya da fasaha na majalisar dattijai na kasa irin wannan matsala.
Sannan kuma ya samu natsuwar majalisar shirya daukar matakin kawo karshen wannan matsalar.

Farfesa Joeffry, ya kara tabbatar da kudirin Cibiyar na samar da ingantattun kayayyakin amfanin gona kamar takin zamani da iraruwar shuka da magungunan kashe kwari da dai sauran su.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog