Al’umma na cigaba da bayyana kaduwarsu da tashin wasu tagwayen ‘Bom’ a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tagwayen bom din sun tashi a ranar Alhamis a tsakiyar birnin Maiduguri wanda ya tai ga mutuwa ga raunuka fiye da 15.
Kazalika rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta hannun kakakinta, Muhammad Aliyu ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Tagwayen bam din sun fashe a unguwannin Mairi da Gwange duk a cikin garin Maidugurin, da yammacin ranar Alhamis a lokacin da Musulmi ke shirin Sallar Layya.