Falala 8 ta ranar Arfat – daga Sheikh Hamza Uba Kabawa

dakikun karantawa

Babban limamin masallacin Juma’a, Sheikh Hamza Uba Kabawa ya fadakar da al’umma wasu taril falala har 8 ta ranar Arfat.

Shehin malamin bayyanawa DABO FM mecece ita wannan rana ma tun da fari? “Ranar Ar’fa rana ce mai girma da daraja da falala. Rana ce da Ubangiji yake shelanta ta a sama. Yake yiwa Mala’aku tinkaho da ita. Ya nuna musu alhazzai da suka zo daga ko ina a sun duniya. Sannan ya sa su a matsayin su zamo sheda cewa ya gafarta musu dukkan zunubansu.”

Banda wannan, ranar Ar’fa tana da darajojin da falaloli da suka hada da :-

1- Rana ce ta kammalawar addini da cikar ni’ima akan bayi , saboda a ranar ne Allah ya sauka da fadinsa ” A wannan yini na cika kammala muku addininku , na kuma cika ni’imata a gareku , na yardar muku da musulunci a matsayin addini ” Al’maida

2- Rana ce ta idi ga wadanda suka tsaya a can.
Saboda fadin Manzon Allah ” Ranar Ar’fa da ranar layya da kwanakin Minna – wato sha daya zuwa sha uku ga sallah- Ranaku ne na Idinmu Musulmi “

3- Rana ce da Allah ya rantse da ita , kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira a riwayar Tirmizi cewa Manzon Allah ya fassara يوم الموعود da Alkiyama. ” المشهود kuma da ranar Ar’fa. ” االشاهد ” ranar Juma’a.

4- Abdullahi ɗan Abbas ya fassara الشفع da Ranar layya. الوتر kuma da Ranar Ar’fa.

5-Azumi a Ranar Ar’fa ga wanda bai tsaya a filin Ar’fa ba yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da wacce zata zo.

6-Rana ce ta gafarar zunubi da ‘yan mutane daga wuta.

7-Addu’a Ranar Ar’fa ita ce mafificiyar addu’ar.

8- Mafi alherin abin da ake so a fada a ranar shi ne ,: لا اله الا الله وحده لا شريك له ، له الملك وله الحمد وهو علي كل شئ قدير 
Mutun zai iya dukkan abin da ya sawwaka na Zikiri.
Wannan falalar bata keɓanci wadanda suke filin Ar’fa ba , a ra ayin wasu daga cikin Malamai.

9-Ita ce Ranar da Allah ya riki alkawari daga dukkan mutane cewa za su bauta masa shi kadai. 
Wannan ya faru ne tun kafin a halicci mutane. Wato ىوم السنت بربكم kamar yadda ya zo daga Ibn Abbas a riwayar Ahmad.
Allah ya datar da mu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog