Labarai

Ban zagi Buhari ba, ban kuma ce ya gaza ba – Hon Gudaji Kazaure

Wanarabul Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalissar tarayyar mai wakiltar karamar hukumar Gwiwa/Roni/Kazaure/‘Yan Kwashi na jihar Jigawa, ya karyata labaran da ake ta yadawa akan ya soki shugaba Buhari.

Hon Kazaure ya nesanta kanshi biyo bayan wani faifan bidiyo da yace ana yadawa akan cewa ya bar tafiyar shugaba Muhammdu Buhari, har ma ya nemi ya sauka tinda bazai iya ba.

DABO FM ta binciko Hon Gudaji a wani bidiyo da ya wallafa a shafinshi na Instagram, yana cewa; “Ana yada bidiyon ne domin a batamin suna.”

“Bidiyon da nayi ne akan sake nada Gwamnan CBN da shugaba Buhari yayi, inda nake kalubalantar sake nadinshi da akayi.”

“Masu wallafa bidiyon sun gyarashi tare da ciccire wasu wuraren saboda karya.”

“Ni Muhammad Gudaji Kazaure, har yanzu ina tare da Shugaba Buhari, kuma bazan daina ba domin tin shekarar 2003 nake tafiyar shugaba Buhari.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Hon Gudaji Kazaure ya baiwa Buhari da gwamnoni shawarar ciyar da al’umma

Dabo Online

APC ta kori Hon Gudaji Kazaure

Dabo Online

Sabon Cajin Banki, fashi da makami ne – Hon Kazaure

Dabo Online
UA-131299779-2