An fanso dan Majalissar jihar Kaduna awanni kadan bayan anyi garkuwa da shi

Yan bindigar da suka sace dan Majalissar dokokin jihar Kaduna, Suleiman Ibrahim Dabo, sun sake shi awanni kadan bayan sun sace shi a titin Kaduna-Zaria.

Rahotanni a jiya Juma’a sun tabbatar da sace Sulaiman Dabo, dan majalissar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Zaria.

Wata majiya mai kusanci da dan majalissar wacce ta bukaci ya boye sunanta bisa rashin umarnin yin magana da dan majalissar, ta shaidawa Jaridar Daily Trust cewa; “Yan Bindigar sun sace dan majalissar.”

DABO FM ta tattaro cewa; Majiyar ta tabbatar da an biya kudin fansa, sai dai bata fadi adadin makudan kudaden da yan Bindigar suka karba ba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.