Labarai

Tsohon Kakakin Majalissar Kano, Yusuf Ata ya kawowa zaman lafiya a unguwar Fagge cikas

An zargi tsohon Kakakin Majalissar Dokokin jihar Kano, Yusuf Abdullahi Ata, da yunkurin yiwa zaman lafiyar karamar hukumar Fagge barazana.

Rahotanni da muka samu daga karamar hukumar Fagge ta jihar Kano, sun zargi Yusuf Abdullahi Ata, a matsayin wanda yasa aka hana Bikin Hawan Kara da matasan unguwar suka saba yi duk shekara.

A cewarsu; Wasu daga cikin matasan unguwar sunyi ta cewa “Yanzu sai mugani ko Wuta Sallau zai hana”

An dai shirya gabatar da Hawan Dokin Kara a unguwar Fagge, a ranar Lahadi, 1 ga watan Satumbar 2019 kamar yacce kungiyar Raya Al’adun Gargajiya ta Matasan Fagge ta bayyana.

Wannan shine karo na 2 da ake zargin tsohon dan Majalissar da kawo wa bikin cikas, domin ko a shekarar da ta gabata, 2018, an zargi Yusuf Ata da yin amfani da matsayinshi na Kakakin Majalissar Kano wajen kama Matasan unguwar da suka shirya bikin.

Tin daga wancen lokacin zuwa yanzu ba’a san musababbin sawa a kama masu shirya bikin ba.

Sai dai wata majiya ta tabbatarwa da DABO FM cewa; Kamun yana da dangantaka da hana ‘dan gidan Yusuf Ata zama Sarki a hawan Karar da aka shirya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ɗan gidan Tsohon Kakakin Majalissar Kano, Yusuf Ata ya makantar da wata Budurwa – Mutanen Fagge

Dabo Online

Sulhun shafaffu da mai a karamar hukumar Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2