Barcelona taci moriya ganga, tace Messi zai iya kama nashi wuri a karshe kakkar bana

Kulob din Barcelona ya furta cewa dan wasa Lionel Messi zai iya barin kungiyar idan kwantirajinshi ya kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Shugaban Kungiyar, Josep Maria Bartomeu, ne ya sanar da hakan a wata hirarshi da gidan Talabijin na kungiyar. – Sashin Hausa na Legit ya tabbatar.

“Leo Messi ya na da kwantiragi har kakar 2020 zuwa 2021, amma ‘dan kwallon ya na iya tashi.”

Bartomeu ya bayyana cewaa kungiyar ba ta fargabar a wayi gari dan wasa Lionel Messi, ya bar kungiyar.

“Leo Messi ya na iya barin Barcelona kafin kakarsa ta karshe.”

Sai dai masana a harkar kwallon kafa suna yiwa kalaman shugaban kungiyar a matsayin kalaman “Anci moriyar Ganga”

Dan wasan dai ya fito a cikin jerin mutane 3 da suka fafata a gasar gwarzon dan wasan duniya da hukumar FIFA dake shiryawa duk shekara.

Cristiano Ronaldo da Virgil van Dijk ne zasu kara da dan wasa Lionel Messi dan kasar Argentina.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.