Duniya

Gwamnatin kasar Indiya ta kaddamar da fara siyarda Audugar Mata akan Rs1 (N5.07)

Gwamnatin kasar Indiya ta kaddamar siyar da Audugar Mata akan kudin kasar na Rupee 1 kacal, kwatankwacin Naira 5.07.

Kasar ta rage farshin Audugar daga Rs 2.50 zuwa Rs 1 domin taimakawa dukkanin mata a kasar su mallaki tasu audugar.

Ministan kula da harkokin Sinadarai (Chemical), Mansukh Mandaviya, ne ya jagoranci shirin a watan Agusta a babban birnin New Delhi dake kasar.

Sai dai wani hoto da Ministan ya wallafa a shafinshi na Twitter ya sha suka bisa dalilin rashin ganin ko mace guda 1 a taron kaddamar da shirin, inda wasu ke ganin ba a daraja Mata da aka saka Maza a abinda bai shafesu ba.

DABO FM ta binciko cewa; Gwamnatin ta kirkiri kamfanin sarrafa Audugar mai suna Suvidha, tin a watan Yulin shekarar 2018, inda a lokacin ake siyar da Audugar akan kudi Rs 2.50 (N12.67).

Binciken DABO FM game da Mata a Indiya;

Zuwa yanzu, Mata miliyan dari 3 da hamsin da biyar ne suka kai minzalin yin Al’ada a kasar.

Kashi 82 daga cikin matan suna amfani da hanyoyin yin amfani da tsumma, kunzugu, kasa, toka da ciyawa domin tare zubar jinin Al’adar da sukeyi.

Adadin da ya kai miliyan dari biyu da casa’in da daya da dubu 100 ne basa amfani da Audugar Mata a kasar ta Indiya.

Sukar da akayi akan kaddamar da shirin da Maza sukayi ba Mata ba

Karin Labarai

Masu Alaka

An fara kama matasan Arewa da Hodar Iblis a Indiya

Dabo Online

Zaben Indiya: Mutum miliyan 900 zasuyi zaben Firaminista a kasar Indiya

Dangalan Muhammad Aliyu

Bidiyo: Gwamna a Indiya, ta kunyata ma’aikaci akan kashe N2550 ba bisa ka’ida ba

Dabo Online

Gwamna a Indiya ya tilastawa jami’an Gwamnati hadawa marasa galihu kudin zaman gida

Dangalan Muhammad Aliyu

Indiya: An kama dan Najeriya da Hodar Iblis “Cocaine” a kasar Indiya

Dabo Online

Jami’an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

Dabo Online
UA-131299779-2