Labarai

Bata-garin mabiya Kwankwasiyya sun yi wa Sheikh Pantami ihun ‘Bamayi’

An zargi wasu Matasa mabiya darikar Kwankwasiyya da yiwa Ministan Sadarwar Najeriya, Dr Isa Pantami, ihun ‘Bamayi’ a jihar Kano.

Hakan na zuwa ne dai dai lokacin da akayi kacubus tsakanin Ministan da mabiya Kwankwasiyya a filin jirgin Mallam Aminu Kano a yayi rakiyar dalibai 105 da Kwankwasiyyar zata tura kasar Indiya.

Bidiyon faruwar al’amarin ya baza kafafen sadarwa.

Sai dai DABO FM ta bincika cewa; wasu daga cikin mabiya Kwankwasiyya, sunyi kokari nusar da sauran mabiyan dasu dena ihu da sukeyi, har ma akaga wasu na mikawa Malamin hannu domin gaisawa da bashi kariya.

An dai yi kira ga Matasa dasu rika girmama mutane musamman irin Dr Pantami da yake masanin addini da zancen Allah wato Al-Qur’ani.

Comment here