Wana laifi Dr Pantami yayi wa ‘Yan Kwankwasiyya da zasuyi masa ihun ‘Bamayi’ ?

Tin dai a daren jiya Talata bayan fitowar wani faifan bidiyo daya bayyana wasu ‘yan Kwankwasiyya suna yiwa Dr Pantami, ihun ‘Bamayi’ a jihar, ake ta cece-kuce.

Duk da cewa malamin yana rike da mukamin Minista a gwamnatin da ‘Yan Kwankwasiyya suke adawa da ita, hakan baya nufin cewar Malamin dan siyasa ne.

Rike mukami ko matsayi a gwamnati baya wani sashi ne nayiwa kasa hiduma wanda a dokance baya zama siyasa.

Sai dai bayan lalacewar tsarukan kasar, an mayarda duk mai mukami, dan siyasa. A wani lokacin har ma cikakken ma’aikacin Gwamnati ba’a kyale ba.

Menene laifin Sheikh Pantami?

DABO FM ta tattaro cewa; Sheikh Pantami Malamine na addinin musulunci wanda aka sanshi da iya bayani da taimako wajen fahimtar da mutane akan aiki na yada addinin Allah.

Masu Alaƙa  Rigar 'Yanci: Kwankwasiyya Farfagandiyya Limited, kashi na biyu Daga A.M.D

A daya bangaren kuma, gogaggene, fasihi kuma kwararre wajen Ilimin Kwamfuta wanda hakan tasa yau ya kasance Minista a Najeriya.

Sai dai a bangaren ‘yan Kwankwasiyya, tin lokacin da Malamin yayi wani karatu akan Kadaita Allah, anan ne yayi misalin kalmar ‘Jahilci’ da wata maganar madugun Kwankwasiyya.

Har ma ya bayyana cewa; “Wanda zai fadi wannan, ko sharar Masallaci bai kamata yayi ba.”

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.