Labarai

Akwai lauge cikin nadi a batun tsige shugaban karamar hukumar Zaria -Sarkin Gandun Zazzau

Wani jigo a jama’iyyar Apc kuma shugaban al’umma a karamar hukumar Zaria Jihar Kaduna, Alhaji Sama’ila Musa Sarkin Gandun Zazzau, ya bayyana matakin da wasu kansilolin karamar hukumar suka dauka na shirin tsige shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim a matsayin son rai da son zuciya maras amfani da kuma ba zai haifarwa Zaria da mai ido ba.

Ya bayyana haka ne a zantawar sa da manema labarai, ciki har da Dabo FM a Zariya.

Ya bayyana matakin a matsayin kin san ci gaba, duk da cewa shugaban karamar hukumar yana damawa da su a sha’anin gudanarwar sa.
Ya ce, wasu su, sun karbi kwangiloli na miliyoyin naira, amma har zuwa yau sun kasa kammala ayyukan da aka ba su.

Ya kuma kwarmata wasu bayanan sirri na kwangiloli da wasu kansilolin suka amsa a gundumomin su.
Da suka hada da wanda aka ba kansila mai wakiltar mazabar Gyallesu ta kamfanin sa mai suna Minister farms enterprises, da aka bashi kwangilar sama da naira miliyan 4, sai kamfani mai suna Tambaya farms mallakin kansilar Dambo, da aka bashi kwangilar sama da naira miliyan 4, akwai kamfani mai suna Cdrigins Nigeria limited mallakin kansilar Anguwar Fatika, da aka bashi kwangilar sama da naira miliyan 4, sai kuma kamfanin Jassim Engineering limited mallakin kansilar Tudun Wada, shi ma da ya samu kwangilar sama da naira miliyan 4. sauran sun hada da Zakmad Global concept limited mallakin kansilar Kaura, da aka ba shi kwangilar sama da naira miliyan 4, shi ma kansilar Tukur-tukur ya amfana da kwangilar sama da naira miliyan 8 da aka ba kamfanin sa mai suna Shanono Ventures limited. Kazalika akwai kamfanin mai suna Mai kwando Global investment mallakin kansilar Kufaina, shi ma da ya amfana da kwangilar sama da naira miliyan 8.

Sarkin gandun na Zazzau, ya sake nanata bukatar da ake ma zababbun kansilolin su koma gundumomin su domin aiwatar da ayyukan raya kasa, mai-makon su koma suna fada da bangaren zartaswa.

Da ya juya ga bangaren dokoki kuwa, ya kalubalance su ne na rashin yin wata doka ta musamman domin amfanar da al’umma.

Ya bukaci masu kokarin kawo husuma su guji hakan, kuma su bari karamar hukumar Zaria ta amfana da romon damokradiyya daga shugaban karamar hukuma da gwamban Jihar Kaduna da kuma shugaban kasa Buhari.

Ko a baya, Mai martaba Sarkin Zazzau da kan shi, ya jagoranci zaman dai-daitawa tsakanin bangaren zartaswa da na dokokin karamar hukumar, amma duk da haka, wasu suka fandare kuma suka naimi komawa da hannun agogo baya. Inji Alhaji Sama’ila Musa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ranar Tarihi: Shugaban karamar hukumar Zariya ya gabatar da kasafin shekarar 2020 a gaban Kansiloli

Mu’azu A. Albarkawa
UA-131299779-2